Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Limamin juma’ar na Tehran wanda yake jawabi a bangare na biyu na hudubarsa ya yi ishara da zagayowar makon dakarun sa-kai na Basij dake tafe, yana mai bayyana cewa; dama ce da ya kamata a yi amfani da ita, domin bunkasa wannan irin tunani da sadaukar da kai a cikin al’umma.
Har ila yau Hujjatul-Islam wal-Muslimin Haj Ali Akbari ya yi ishara da irin sadaukar da kan da al’ummar Iran su ka yi, yana mai ambaton mutane irin su shahid Mustafa Chamran, Shahid Kassim Sulaimani, haka nan kuma Imad Mugniyah na kungiyar Hizbullah ta Lebanon.
Limamin na Tehran ya kira yi masu wakiltar Iran a tattaunawar Nukiliya da su kasance tare da wannan irin tunanin na dakarun sa-kai-Basij.
342/